Amsoshin Tambayoyin da Barrister Bulama Bukarti ya Aikewa da Kungiyar Izala ta Jihar Kano (3)

(Wanda bai karanta rubutu na 1 da na 2 ba, yanada kyau ya koma ya karanta, rashin karantawar zai hana shi ÿancin yance hukunci).

TAMBAYA TA BIYU: Annabi SAW ya kauracewa Nana A’isha a lokacin da ake tuhumarta, to a ina su Mallam suka samo sunnar kusantar Ganduje a lokacin da ake tuhumarsa?

AMSA: Gaskiya ne, Annabi SAW ya kauracewa Ummuna A’isha R.A a lokacin da munafukai suka jefeta da aikata alfasha, amma wannan ba zai zama dalili akan cewa dukkan mai lefi ne shari’ah ta wajabta a kaurace masa ba, na fadi hakan ne saboda dalilai kamar haka:

1. Ita Nana A’isha mata ce ga Annabi SAW, sai ake tuhumarta da aikata alfasha ‘Wal Iyazu Billah’, to a matsayinsa na mijinta wanda bai san gaibu ba, dole ne zai kaurace mata, saboda kusantarta zai zamanto matsala, koda wata mu’amala ta auratayya ta gudana tsakaninsu, kuma Allah ya kadarci samun wani rabo, to wannan rabon zai zamanto abin yiwa zargi da yar da magana, musamman a wajen munafukai…

2. Abinda zaisa mu fahimci cewa kauracewar da yayi mata yayi ne a matsayinsa na mijinta shine: bai yiwa kowane musulmi umarnin ya kaurace mata ba. Shiyasa a hadisin bamu samu mahaifiyarta da mahaifinta da sauran mutane sun kaurace mata ba.

3. Inda ace kaurace mata hukunci ne gamamme, da mahaifinta, wanda yake shine mutum mafi girma a duniyar musulunci bayan Annabi SAW, da ya kaurace mata, saboda yafi kaunar Annabi SAW fiye da ita.

4. An saukar da hukuncin kauracewa akan sahabbai guda uku da suka ki zuwa yaqi, KA’AB BN MALIK, HILALU BN UMAYYATA da MURARATU BN RABI’E, amma dayake su nasu hukuncin gamamme ne, daga kan Annabi SAW har zuwa kasa, babu wani mahalukin da yake kusantarsu, koda kuwa ta hanyar cinikayya ne. Don har daga karshe ma akayi umarnin matansu su fice sukoma gidajensu. Saboda nasu hukuncin gamamme ne.

5. Ta yadda zamu kara gane cewa ba akan kowanne abu yake zama wajibi a kauracewa mutum ba, ai idan muka tuna, zamu ga cewa an samu wasu cikin wadanda suka rayu da Annabi SAW, wasu sunyi zina, wasu sun sha giya, wasu sunyi sata, da makamantansu, toh Barista ai kaga wannan ba tuhuma bace, tabbas ne ma, amma ba’a yiwa al’umma umarnin su kaurace musu ba.

In short, ba akan kowanne laifi ake kauracewa mutum ba.

A NAN INASO NACE WANI ABU…

A fahimtarmu har yanzu muna a level ne na TUHUMA, koda a yaren su Barista, sai de ace ‘ana tuhumar Gwamna…’ ita kuma tuhuma a musulunci ma umarni akayi mana da yiwa masu imani kyakkyawan zato akanta, mu guji saurin yarda da ita. Duk wanda ya nazarci ma’anonin ayoyin da suka sauka domin Wanke Nana A’isha, zai fahimci hakan. (a duba farkon Suratun-nur).

Sannan wani abu da ya bani mamaki, Dr. Pakistan acikin jawabinsa yake cewa ai dama an tuhumci Nana Aisha da kuma Annabi Musa, sai Barista yake ganin kamar Dr. Ya kamanta Nana Aisha da Annabi Musa da Ganduje, amma kuma sai ga Barista yana hada alaka ta hanyar basa misali da kauracewar Annabi SAw ga Nana A’isha da kuma rashin kauracewar Izala ga Ganduje. Toh muma muna da tambaya:

Menene hikimar hada wannan misalin?

Shin Barista yana kamanta Manzon tsira ne da Pakistan?

Zamu cigaba nan ba da dadewa ba insha Allah.

Awaisu Al’arabee Fagge
Chairman, Jibwis
Social Media
Kano State.
28-11-2018

8 comments

 • Wannan shine tufka da warwara am muku tambaya maimakon amsa sai dubule kuke, Allah ya sauwaka

 • Wallahi gabada magannganunka basada wata alkibla sai tafka-tafka kakeyi har yanzu baka bada amsa daya cikakkiya ba, kawai kace malam yaje ya karbo kasonshi shima

 • Allah ya sawwaqe muku, Allah ya shirya mana malaman wannan zamani, Allah ya yaye musu kwad’ayi!

 • Shamsuddeen salisu tashena

  Kai Allah dai ya sawwake. Nifa har yanzu ban gamsu da amsar nan da suka bayar ba. Kamata yayi ace shi shugaban izala ya fito da kansa yayi jawabi ya kuma wanke kansa saboda ana magana ce ta ilimi da kuma fahimta anan wajen. Gwamna dai dole ace yayi kuskure koda ba’a tabbatar da zargin da ake masa ba. Saboda ga bidiyo kiri kiri nan wanda ko makaho zai iya jin maganganu kuma ya gamsu. Allah dai ya kyauta

 • Wlhi duk wanda bai gamsu da wadannan hujojin ba jahili ne ba maison gaskiya bane. Garama Ku dakata da amsa musu tambayoyin Dan naga masu comments basason gaskiya Allah yasawake acema Qur’ani, Aya kace baka gamsu ba.

 • Kwadayi ya sa malamai rufe ido wajen fadar gaskiya

 • Abdulkarim Muhammad Auwal

  Kaji tsoron Allah, wajibi ne ga kowanne mumini yayi koyi da Annabi صلى الله عليه وسلم sai dai a inda yake shakhsiyya ce tasa. Idan kaura cewa Wanda ake tuhuma sunnar sa to lallai dole mu kaurace masa, idan kuma kusantarsa ake so ayi to lallai mu kusance sa.
  Al’amarin yadda yake:
  Ana tuhumar mutum Ku kuma kuka kusance shi don Ku jajanta masa har kuke mass matashiya da manyan bayin Allah, ka mata yayi ku bari a wanke shi sai kuyi masa hukuncin wanda aka yiwa kazafi kuje Ku jajanta masa ko kuma a tabbatar da zargin sai Ku duba a shari’ah laifinsa na a kaura ce masa ne ko kuma na a kusance shi ne, amsa na ga malamai su duba nassoshin da ka kawo da masu da aikin sahabbai don samun mafita.
  Allah ya shirya mu, ya bamu ikon karbar gaskiya da aiki da ita koda daga na kasa da mu ne a ilmi da daukaka.

 • Umar Mushaffau zubairu

  Allah ya rabamu da kwadayi, wannan kaskantar da qungiyar izala ce kun nuna son duniya kuru kuru wallahi barrister yafiku hujja kun kasa amsa komai

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.