Amsoshin Tambayoyin da Barrister Bulama Bukarti ya Aikewa da Kungiyar Izala ta Jihar Kano (2)

Tanbihi:
1- Duk wanda bai karanta rubutun farko ba, to zaiyi kyau ya koma ya bibiya. Rashin bibiyar zai hanaka fahimtar sakon yadda yakamata.

2- Ban shardantawa kaina amsa tambayoyin Barista kamar yadda yayisu ba, saide zan fara dauko mafi muhimmanci daga cikinsu ne, koda ba dasu ya fara ba.

JIBWIS

TAMBAYA TA DAYA: Menene hikimar kawo misalin Kazafin da aka yiwa Nana A’isha RA da Annabi Musa AS? Ko malam yana kamanta Nana A’isha da Annabi Musa ne da Ganduje? Sannan hakan bai yi kama da abinda Malam Jafar yayiwa raddi ba a lokacin da aka kamanta jifan da aka yiwa Annabi SAW a Da’ef; da kuma wanda aka yiwa Atiku a Kano???

Amsa: Da farko dai muna cewa: أعوذ بالله من الشيطان الرجيم, Allah ya tsari Dr. Pakistan da kamanta Annabi Musa da Nana A’isha da ganduje, nisan dake tsakaninsu yafi nisan sama da kasa. Haba mal. Bukarti! Ai koda an saba da Dr. akan ra’ayin siyasa ai ya kamata ayi masa kyakkyawan zato…

Sanannen abu ne cewar mutane sukan bawa junansu hakuri ta hanyoyi daban-daban, daga ciki, akan tunawa mutum wani abin damuwa ko matsala da ya samu wadanda suka fishi girma da matsayi.

Misali, Idan wani malamin yaje yayi wa’azi mutane suka ki karba, sai a bashi hakuri ace masa ka tuna cewa Annabi Nuhu ma yayi shekara 950 yana wa’azi amma mutane ÿan kalilan ne suka karba. Yayin da kake wannan misalin; babu wani mutum mai adalci da zai jefeka da cewar ka kamanta wannan malamin da Annabi Nuhu AS. (هذه بتلك ).

Wannan shi yasa ake yiwa wadanda suka gamu da bala’in rashin lafiya wa’azi da abinda ya sami Annabi Ayyuba, ake yiwa wanda ya hadu da bala’in batan d’ansa wa’azi da abinda ya sami Annabi yaqub, ko ayi wa’azi ga wanda ya hadu da bala’in hassadar yan uwa da abinda ya sami Annabi yusuf…

Bawai dan a kamantasu da wadannan manyan bayin Allah ba a’a saide don a rage musu radadin musifar da ta same su ta hanyar nuna musu hakan ya taba samun wadanda sukafi su daraja da alkhairi.

Shi yasa ko a lokacin da malam yake magana ya ce ai an tuhumci wadanda sukafi gomna daraja a wajan Allah da kuma wajan duk wani musulmin kirki, dan haka kirkinka, ko tsoron Allahn ka bai iya hana a jefa maka tuhuma ko ta gaskiya ko ba ta gaskiya ba, dan haka babu laifi a musulunci idan wani abin damuwa ya sami mutun a bashi hakuri ta hanyar tuna masa abinda ya taba samun wanda ya fishi daraja mai kama da abinda ya sameshi.

Dangane da amsar Marigayi Sheikh Ja’afar Allah yayi masa rahama, ga wadanda suka fadi abinda suka fada gameda abinda aka yiwa Atiku, in Barista zai tuna abinda aka dinga fada wanda kuma Sheikh Ja’afar ya bada amsa a kai, abinda akace shine ‘an jefi Atiku kamar yanda aka jefi Annabi, shine malam ya yi tir da waccan kamancceceiya da ya fahimta ana kokarin yi, tsakanin Annabi SAW da Atiku , wal-iyazu billah. Ala kulli halin, misalan da muka bayar sun isa su fayyace niyyar Dr. Pakistan a jawabin da yayi.

Zamu tashi a tambaya ta biyu nan ba da jimawa ba insha Allah.

Awaisu Al’arabee Fagge
Chairman Jibwis Social
Media, Kano State.
27-11-2018

6 comments

 • Allah ya biya

 • Kwata Kwata wannan amsar batayi bah, ta yy mtm zai aikata laifi. Sannan kuma a rinqa nuna cewa kmr mah rarrashinsa akeyi??? Har a rinqa qoqarin buga misali da auliya’u llah?

 • Bara'u Khalid Usman

  To, Alhamdu Lillahi. Amma ni a fahimtata, ba a wannan gabar ya kamata Malam yayi magana irin wannan ba, domin kuwa wannan gabace ta zargi wacce a Muslinci bincike ake yi, ba goyawa wanda ake zargi baya ake ba. Kamar yadda Allah yake cewa: يايهاالذين ءامنوا ان جاءكم فاسق بنبأ فتبيواان تصيبواقوما بجهالة فتصبحوا على مافعلتم نادمين. Sabo da haka, kamata yayi Malam ya taimaka a binciki gaskiyar zargin ko da ya babatar wannan zargin karyane. Sannan idan Gaskiya ta bayyana, karyar zargin ta tabbata, to sai Malam ya zo yayi irin wadancan bayanai dan hakurkurtar da wanda aka zarga. Amma abin da Malam din yayi a yanzu, a fahimtata kuskure ne. Domin kuwa da kamar a ce wani daga cikin Malaman darikane yayi hakan, to da watakila kaji su Malam ko dalibansu suna cewa kwadayine. Allah ya ganar damu Gaskiya ya kuma bamu ikon binta da goya mata baya, Ya kuma ganar damu karya ya bamu ikon kauracemata. Amin.

 • Allah ya karawa malamanmu sani da aiki da, muna goyan bayan malam Allah ya karbi ayyukansa na alheri ya gafarta korakoransa. Saidai awannan gaba malam ya goyi bayan gobna kamata yayi ya fadi irin maganar daurawa na cewa ayi bincike a gano gaskiya sannan a hukunta mai laifi

 • Abdulkarim Muhammad Auwal

  Hmmmmm Malam Al’arabee baka amsa tambayar nan ba, wayannan Misalai da ka bayar basu haulayi ba. Nana Aisha al’amarinta kazafi ne Allah ya wanke ta, sai ka jira Ganduje in an wanke shi sai ka kawo masa misali da ita (رضي الله عنها)
  Malami mai wa’azi don’t kayi masa nasiha akan hakuri kayi mass ishara da Annabi Nuhu عليه السلام kayi dai dai saboda akan tafarkin gaskiya suke dukansu.
  Malam muji tsoron Allah my amsa kuskuren mu, mu nufi Allah akan wadannan al’amura. Mu guji goyon bayan azzalumai, mu guji fada da junanmu akan azzaluman shuwagabanni.
  Ina matukar takaici ace fadan Malamanmu ya zama akan kare azzaluman shuwagabanni, Da Dr. Sale Pakistan da Dr. Gumi a fahimtata duk abinda suka aikata ba dai dai bane. Akwai al’amuran da suka fi wadannan muhinmanci ga mai Da’awa.
  Allah yasa mu gane. Amin

 • Kuma kamar yadda Barrister ya tambaya, idan ban mance ba, ai ya faɗi wani abu a kan video. Shin Nana Aisha , da Annabi Musa, an saamu wani video wanda yake tabbatar da abinda aka tuhume su da shi ko kuwa? Sabida haka Inaga lallai wannan amsar da aka bayar baza ta cika ba matuƙar Malaman basu goge wannan tambaya da Barrister ya yi ba akan video

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.