Amsoshin Tambayoyin da Barrister Bulama Bukarti ya Aikewa da Kungiyar Izala ta Jihar Kano (1)

Bismillahirrahmanirrahim.

Bayan haka, mun saurari wadansu tambayoyi guda 16 da Bar. Bulama Bukarti ya aikewa kungiyar Izala ta jihar Kano, da shugabanta, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan, akan ziyarar da Kungiyar ta kaiwa Mai girma Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Hakan yasa muka dauki haramar mayar da amsoshi ga Bulama, domin ya waraka, kuma al’umar da suke da bukatar amsoshin da yayi suma su waraka.

JIBWIS

Amma kafin mu shiga bayar da amsa; muna da wadansu bayanai masu muhimmanci kamar haka:

1. Muna yabawa da godewa Bulama Bukarti, musamman yadda yayi amfani da usulubi da mai cike da girmamawa da mutuntawa ga shugabanmu, duk dayake baristan baya goyon bayan abinda shugaban namu yayi. Wannan abin a yaba ne. Mun gode.

2. Kasancewar Barista Bulama yace yayi tambayoyinsa ne ga Dr. Pakistan da kuma Kungiyar Izala Ta jihar Kano, sai muka ga rashin dacewar shigowar Dr. Pakistan domin bayarda amsar, domin dalilai kamar haka:

A) Barista bulama ya shigo ne bayan musayar sakonni tsakanin Dr. Pakistan da Dr. Gumi, kenan ba da shi akeyi ba, to bai dace ace Dr. Pakistan ne zai bashi amsa ba.

B) Barista Bulama ya tura sakonsa ne a Social Media, Mu kuma mune muke magana da yawun kungiyar Izala a social media, kenan hurumin mu ne mayar da martani akan wannan batu, musamman dayake ni shugaban Social media din, da ni akaje waccan ziyara.

C) Dayake Bulama Bukarti lauya ne, nasan yana da masaniya akan cewa ‘wani yakan iya kare hakkin wani, ya kan iya amsa tambayoyi a madadin wani, koda kuwa a fanni shari’a ne kotu’. Toh bukatar amsoshi ake, ko da daga bakin wanene, ba lallai sai Dr. Pakistan ba.

D) Ko da kasancewarmu ÿan social media bai bamu hurumin amsa wadannan tambayoyi ba, duk da haka akwai lemar da zamu iya fakewa, domin kuwa ni da nake rubutu, ina cikin EXCO na kungiyar izala a matakin jihar Kano, kuma tambayoyin da Barista yayi, yayisu ne ga Dr. Pakistan da kuma kungiyar Izala baki daya.

Da dan wannan tanbihi nake neman taimakon Allah wajen fara amsa tambayoyin Barista.

TAMBAYA TA FARKO DA KUMA AMSAR TA……..

(Zamu tsaya anan, amma zamu cigaba anan gaba kadan, domin gudun yin rubutu mai yawan da zai wahalar da mai karantawa)

Awaisu Al’arabee Fagge.
Jibwis Social Media
Kano State.
26-11-2018

13 comments

 • Farouk Usman Zunnurain

  Hmm ai mu wajen karatu bamu gajiya wa Akhramakallah kamata yayi a wayar mana da kai domin fita daga duhu

 • Wannan ai ba amsa ba ce, Kuma Wanda yai rubutun ma fa wani Dan karamin yaro ne, ta Yaya ze iya amsa wadancan tambayoyin? No na San shi shi ma ya San ni, na kuma San ba ze iya amsa tambayoyin da Barrister yai ba. Sabida haka Awaisu Kai hakuri ka bari shuwagabannin ka su amsa wannan wajen ba irin musun da ka Saba yi da abokan ka ba ne

 • Kamal masisi gumel

  A temaka a karasa mana amsoshin tambayoyin barr.

 • Muhammad Salihu Isa.

  Gaskiya ya kamata Kungiyar Izala bisa Jagorancin Shigubanta Dr. Pakistan su ba da amsar Tambayoyin da Barista yayi musu domin wannan abin da nake gani baiyi kama da amsa ba.

 • Abdullahi Aminu Abdullahi

  Muna saurare

 • Zaharaddeen zakariya'u

  Plx Ae baxamu gajiba da karantawa muddin ka bada amsoshi da hujjoji gamsassu, Don haka juna jiranka, kasancewarmu ‘yan Ahlussunah bazai sanya mu kauda edonmuba daga fadin gaskia edan munga Anyi kuskure…
  Allah muna riqonka kabamu ekon gane gaskia gaskiace mubita kuma mugane Qarya Qaryace domin mu Gujeta…Ameen

 • Ay ita gaskiya dayace amsa kawai zaka bayar,ba magana mara ma’anaba bulama tambaya yayi kawai mu kuma muna jiran amsa

 • Mubarak Usaini Megi

  Muna saurare tare da bibiya…..

 • Mustapha Abdullahi

  Tsabar rashin San gaskia ne sbd an fadawa shugabanku yayi kuskure Akan abinda yayi tambayoyi guda 16 ya zakai dasu? Dan ka kare kanka ai dole wani idan ka fadi gaskia wani sai ka sirka ta da karya ko San zuciya kawai ka yarda kayi kuskure shikenan a wuce wajen da Jin kunyar Lahira gwara ta duniya

 • Wannan ai Magana ce tabanza

  Meyasa Bai aikaku ku kuje kukai ziyarba indai har bazai iya amsa tambayarba?

 • Bawan Allah ka amsa tambayoyi kawai banda kame kame gajiya da karatu bawani uzuri bane muba jiranka

 • Ibrahim Yusuf Abubakar

  Da ka shina kai mai rubutu da baka bata lokacinka na wancan rubutun ba, da sai kawai ka wuce kai tsaye kan amsoshin wadancan zafafan tambayoyi da Bakarti ya yiwa Pakistan.

 • To muna dako Amma Kalmar haramun shugaban yan social media daka fada ta dau hankalina Amma muna saura,a video Barista yayi dasai kaima said mu ganka in abun naka ba Maja bane?

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.