Wani dattijo ya nemi Kotu da ta sahhale masa ya rage shekarunsa na ainihi

Wani bawan Allah ya nemi Kotu ta sahhale masa ya rage yawan shekarunsa na haihuwa kamar yadda kafar yada labaran Sky News ta labarto. Dattijon dan shekara 69 mai suna Emile Ratelband yana neman rage shekarunsa ne da shekaru 20 domin ya koma dan shekara 49.

Tsohon ya gurfanar da karamar hukumarsa ne a gaban wata kotu da ke birnin Arnmen na kasar Nezalan bayan karamar hukumar ta hana shi damar canza shekarun nasa. Da ya ke gabarta hujjojinsa a gaban kotu, dattijo Emile ya ce: “tunda doka ta bawa masu son canza jinsunsu daga mace zuwa namiji ko kuma daga namiji zuwa mace, to ya kamata a bawa wanda su ke son canza shekarunsu ma dama.” Idan har aka bashi wannan dama to ya yafe fenshonsa wanda karamar hukumar ke biyan shi.

Emile ya ci gaba da sanar da kotu cewa shi yanzu jin kansa ya ke gangan tamkar dan shekara 45, kuma hatta likitoci sun tabbatar masa da haka domin sun gaya sama cewa yana da karfi kamar dan shekaru 45 din. Ya ce rage shekarun zai bashi dama ya ci gaba da aikinsa. Zai kuma sa ya yi farin jini a gurin mata, kuma ya samu daman siyan motoci na alfarma da manyan gidaje.

Wannan al’amari ya jawo cece-kuce a kasar Nezalan har ta kai wasu sun fara tuhumar lafiyar hankalin dattijon. Ammam alkalin da ke sauraron shari’ar ya ce shi ya fahimci hujjojin Emile kwarai, kuma yana ga in dai har doka za ta bawa mutane dama su canza jinsinsu, me zai hana a bawa masu son canza shekarunsu damar yin hakan? Saidai alkalin yace ya lura cewa bada wannan dama ka iya kawo matsala domin tamkar bawa mutane dama ne su goge wani bangare na tarihinsu.

Kotun ta daga wannan shari’a zuwa makonni 4 masu zuwa domin yanke hukunci.

IMG-4935

3 comments

 • Salisu muhammed Fagge

  Wani aiki sai turawa. Duniya na kwaikwayoku Amma a badini ba a zahiri ba ku da hankali. Allah ya kyauta.

 • Usman Bala Muhammad

  Allah daya gari ban-ban, saboda bin tsari sai ya nemi izini ma unlike a Naija

 • mustaphal Ameen Alhausawiy

  Assalamu alaikum
  HakIka in akai duba da Irin Al adunsu da dabiunsu yana da Gaskiya
  Kuma shi Alkali dazaice yin hakan goge tarihine
  Ai wanda yai daawar canza Halittarsa shine babban mai goge Tarihi kuma YAN bal ma Ai suna canza shekaru KAI dayawansuma Shekarun karyane @ Al-hausawiy

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.