Ga bidiyon da a ciki Lai Muhammad ya ce Gwamnati na kashe 3.5 million duk wata wajen ciyar da Zakzaky

Kamar yadda za ku gani a cikin wannan bidiyo, a minti na 5:36 Lai Muhammad ya ce “Gwamnati na kashe miliyan uku da rabi (3.5 million) duk wata wajen ciyar da shi (wato Zakzaky).

Sai minista sifuri, Rotimi Amaechi, wanda ke zaune a gefen Lai Muhammad ya kutso baki yana mai cewa “In hakane, ni ma a kai ni a garqame”

Daga daganan sai Lai Muhammad ya kada baki ya ce “Gaskiya, kar ku ce na fada, amma gaskiyar abinda ke faruwa kenan.”

Shi ko Amaechi ya amsa da cewa “Ni zan yadda a riqa bani naira dubu dari biyar (N500, 000) duk wata a kiqe ni a gidan kurkuku.”

Sai Lai Muhammad ya ce “ai tambayowa nayi. Amma bana son in tada hankalin mutane”

Source: SaharaTV – https://www.youtube.com/watch?v=D225ZZhNKyw

5 comments

 • mustaphal Ameen Alhausawiy

  RAINAWA MUTANE HANKALI KURUM SUKEYI. NIDAI BAZAN KARA ZABE BA

 • Lai Muhammad kamar kullum baya iya fadar abinda hankali zai kama, amma banyi mamakin haka ba duba ga yadda gwamnatin nan take tafiyar da al’amuranta kawai ana maimaita abinda PDP tayi ne, ta wani fannin ma PDP tafi wannan gwamnatin kokari.

 • Hmm. Allah yakyauta. Yakamata shugabannin Nigeria su sani cewa Akwai hisabi. Ranar Gobe kiyama kobo daya duk wanda yasata zai fito da ita, ranar da mutum bashida shi. Allah yasakamana.

 • Ahmad ibrahim Gwale

  All the time his name reflect his words.

 • Sulaiman bappah

  Lalle kam! Ko magana fa bai iya ba. Ahakan kuma wai ministan yada labarai.

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.