Burtaniya ta Karyata Sojojin Najeriya

Burtaniya ta ce mutum 50 aka kashe a arangamar da aka yi tsakanin ‘yan Shia da jami’an tsaron Najeriya a Abuja a makon jiya, kamar yadda sashi Hausa na BBC ya rawaito. Kafar yada labaran ta ce:

“Sanarwar da wata mai magana da yawun ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya, Louise Edwards ta aike wa manema labarai ranar Lahadi, ta ce kasarta ta bayyana wa gwamnatin tarayyar Najeriya matukar damuwa kan rikicin da kuma yawan mutanen da aka kashe sakamakonsa.

Sanarwar ta bukaci dakarun tsaron Najeriya su rika gudanar da ayyukansu bisa dokokin kasashen duniya da na cikin gida da kuma kare hakkin farar hula.”

Wannan sanarwa ta ci karo da alkaluman da sojojin Najeriya suka fitar na cewa Mutane 5 ne suka rasa rayukansu arangamar da debi kwanaki ana yi.

Saidai Ofishin jakadancin na Burtaniya ya yi maraba da alkawarin da gwamnatin Najeriya ta yi na gudanar da cikakken bincike kan batun da kuma alwashin da ta sha na hukunta duk jami’in tsaron da ya keta doka lokacin rikicin, kamar yadda BBC ta rawaito.

“Rikicin ya fara ne a lokacin da ‘yan Shi’a suka fara tattakin Arbaeen na shekara-shekara a Abuja – wato tarukan tunawa da kisan jikan Manzon Allah (SAW).

‘Ba sa dauke da makamai’

A lokacin tattakin, ‘yan Shi’a sun neman saki jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda ake tsare da shi kimanin shekara uku da suka wuce, bayan wani rikici da kungiyar ta yi da sojoji a Zaria.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta soki gwamnatin Najeriya kan kisan ‘yan Shia, tana mai cewa kisan “mutanen da ba sa dauke da makamai take hakkin dan adam ne.”

Daga bisani rundunar sojin Najeriya ta wallafa wani bidiyon na Shugaban Amurka Donald Trump wanda ta kafa hujja da shi wuri bude wa ‘yan Shi’a wuta.

A cikin bidiyon, Shugaba Trump ya ce sojoji za su iya amfani da karfi kan baki ‘yan ci rani da ke jifansu da duwatsu.

“Idan suka yi jifa da duwatsu… ku dauka sun yi da bindiga ne,” in ji Mista Trump a wani faifan bidiyo.

Rundunar sojin ta goge bidiyon bayan ta sha suka daga wurin ‘yan kasar.”

2 comments

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: